An Karrama Gwarzon Shekara Na Musabukar Kur’ani Ta Kasa A Jiha Da Milyan 10 Da Kujerar Hajji 4
Wani matashi ɗan asalin jihar Sokoto maisuna Nura Abdullahi Bello daga karamar hukumar Wamakko shine ya lashe gasar musabuka hizifi 60 ta kasa wanda a tarihi shine karo na farko a jihar Sokoto da ya samu wannan nasara a wannan matakin.
A jiya ne aka yi bikin karrama shi wanda ya samu halartar manyan mutane da dama hadi da Gwamnan jihar Sokoto Aminu Wazirin Tambuwal da Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alh. Muhammad Sa’ad Abubakar 111 mni.
Kafin kammala bikin Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya bada damar naɗa gwarzon shekarar da sarautar Modibbon Sokoto, sannan Gwamnan Sokoto ya kara gwangwaje shi da kujerar hajji guda hudu da naira milliyan goma da kuma ɗaukar nauyin karatun shi har zuwa matakin PhD a duk jami’ar da yake bukata.
Haka ma Nura Abdullahi zai sake wakiltar Nijeriya a musabakar duniya da za ta gudana a Saudiyya.