An Kashe Naira Biliyan 200 Wurin Shirye-Shiryen Fara Kidayar jama’a
Hukumar Kidaya ta kasa ta bayyana cewa ta kashe naira biliyan 200 wajen shirye-shiryen fara kidayar jama’a da gidaje a kasar nan baki daya.
Naira biliyan 200 din da aka kashe dai somin-tabi ne daga cikin naira biliyan 800 da aka tsara za a kashe kafin kammala kidayar.
Shugaban Hukumar kidaya ta kasa (NPC), Nasir Kwarra ne ya bayyana kashe kudaden a wata ganawa da ya yi da shugabannin kafafen yada labarai, ranar Alhamis, a Abuja.
Kwarra ya ce aikin kidayar ta hanyar na’urar zamani ya yi tsada ne bisa yin la’akari kayan aikin da ake bukatar shigowa da su, sai kuma dimbin data din da ake bukata wajen gudanar da aikin kidayar.
Ya kara da cewa NPC za ta bukaci ma’aikatan kidaya har miliyan 1, domin ganin an gudanar da sahihin kidaya kuma karbabbe a wurin jama’ar fadin kasar nan.
Daga nan ya sha alwashin ganin an gudanar da sahihiyar kidaya cikin nasara. Sannan kuma ya roki kafafen yada labarai su ci gaba da bayar da ta su gudummawa wajen yayata shirin kidayar.
Manajan Ƙidaya Inuwa Jalingo ya ce hukumar ta na aiki ba dare ba rana domin ganin ta cimma kyakkyawar nasarar gudanar da kidayar jama’a ta hanyar amfani da na’urar zamani a cikin nasara.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim