An rantsar da ma su yi ma ƙasa hidima (NYSC) su 658 a Jihar Katsina.
An gudanar da rantsar da ma su yi ma ƙasa hidima (NYSC) kimanin 658 a jihar Katsina
An gudanar da horar da su tare da rantsar da su a ranar Juma’ar da ta gabata.
Majiyar tace, Ƙungiyar Matasa masu yi ma ƙasa hidima reshen jihar Katsina, ta rantsar da Kwafas 658 da aka turo jihar Katsina domin gudanar da aikinsu na shekara daya ga ƙasa.
Babban Alƙalin jihar Katsina, Mai shari’a Musa Danladi Abubakar ne ya rantsar da sabbin ‘yan ƙungiyar a sansanin masu yi wa ƙasa hidima na Katsina NYSC da ke babban birnin jihar Katsina.
Da yake jawabi ga ‘yan ƙungiyar a yayin bikin rantsarwar, Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya buƙace su da su ba da himma wajen ganin sun sanya kyawawan ɗabi’u na haɗin kan ƙasa da kuma ci gaba a cikin shekarar hidimarsu.
Gwamna Masari, ya bayyana ’yan ƙungiyar a matsayin muhimman masu kawo canji, ya kuma gargaɗe su da su tabbatar da cewa a ko da yaushe suna nuna halayen ‘yan Najeriya masu kishin ƙasa wanda a shirye yake ya biya farashi mai tsoka idan buƙatar hakan ta taso.
Gwamna Masari wanda ya samu wakilcin, Hon. Hamza Muhammad Borodo, mai ba shi shawara na musamman kan sha da fataucin miyagun ƙwayoyi da safarar mutane, Hamza Muhammad Borodo, ya tunatar da sabbin ‘yan ƙungiyar cewa, babban zaɓe ya kusa ƙaratowa, kuma za a iya kiransu da su haɗa kai da takwarorinsu da sun riga sun shiga fagen gudanar da zaɓe.
Gwamnan Katsina ya kuma buƙaci ’yan kungiyar da su haɗa kai da ƙoƙarta ma gwamnati a halin yanzu wajen wayar da kan jama’a da wayar da kan al’ummar da suka karɓi baƙuncinsu domin fahimtar wasu sauye-sauyen da aka riga aka kafa.
Tun da farko, Shugabar NYSC reshen jihar Katsina, Hajiya Aisha Muhammad ta yaba wa sabbin ‘yan ƙungiyar bisa yadda suka gaggauta yin garambawul ga rayuwar su a sansanin, tare da nuna ƙwazon fiddo da’a masu kyau a gare su.