An Sace wani firɗeɗen Rago bayan an Sakawa Ragon Suna da Bola Tunubu a Kebbi.
“Wani mai suna Abdulmutallib Garba mai laƙabin suna Buzu, a ƙaramar hukumar mulki ta Shanga Yasiye rago a kasuwar tungar giwa na sama Naira dubu 60, wanda abisani saboda soyayya da ƙaunar da takewa jam’iyyar APC yasawa ragon suna Bola Tinubu.
“Yace, yasan yanada tarin maƙiya, kuma bakowane zaimishi wannan ɗanyen aika-aikanba banda ‘yan Jam’iyyar adawa.
“A ranar Litinin 16 ga watan Janairu nasiye ragon, wanda abisani bayan fallasa jin yadda na raɗawa dabban suna yasa aka banyeshi acikin tsakiyar dare.
“Saidai kuma abun mamaki da Buzu ya iya sanarwa manema labarai yace:-
Shida ƙaninshi kowa yasiyo rago, wanda ƙaninshi mai suna Uzairu ɗan Jam’iyyar PDP ne, yayinda suka siyo dabbobin Uzairu ya raɗawa nashi rago da sunan AMINU BANDE, wato sunan ɗan takarar gwamnan jihar Kebbi a ƙarƙashin tutar jam’iyyar PDP.
“Buzu yace, idan ba ɗan Jam’iyyar adawa ba babu yadda za’a ɗauke mai Tinubu abar Aminu Bande.
“Saidai daga ƙarshe yayi gargaɗi ga Uzairu cewa yayi hani tare da jan layi ga duk wani abokinshi ɗan Jam’iyyar adawa da shigo masu a gida, domin yin hakan nada wata halaƙa da sace mai Bola Tinubu.
“Zaikuma kai rahoto a hukumar ‘yan sanda na ƙaramar hukumar mulki ta Shanga, da idan babu wani martani, zuwa gaba zai iya ɗaukar mataki kan Ahmad Tinubu.
RAHOTO:- Comrade Yusha’u Garba.