Daga Kamal Aliyu Sabongida
An sake zabar wani dan majalisar jihar Pennsylvania da ya mutu a watan Oktoba, Anthony DeLuca a lokacin zaben tsakiyar wa’adi na Amurka.
Fox News ta ruwaito cewa DeLuca ya mutu a ranar 9 ga Oktoba, 2022 “bayan ɗan gajeren fama da lymphoma, cutar da ya yi fama da ita sau biyu a baya.”
Dan majalisar mai shekaru 85 ya kasance dan majalisar wakilai mafi dadewa a jihar Pennsylvania kafin mutuwarsa.
Da suke mayar da martani game da sake zabensa, Jam’iyyar Democrats ta Majalisar Wakilai ta Pennsylvania ta ce, “Yayin da muke matukar bakin ciki da asarar Wakilin Tony DeLuca, muna alfaharin ganin masu kada kuri’a sun ci gaba da nuna amincewarsu a gare shi da kuma jajircewarsa ga kimar Demokradiyya ta hanyar sake zaɓe shi bayan mutuwa.
DeLuca ya kasance mazaunin Penn Hills sama da shekaru 60.
Ya fara tafiyarsa ta siyasa ta hanyar yin hidima a Hukumar Nazarin Gwamnati ta Penn Hills.