Jami’an ‘ya sanda a garin Zaria dake jihar Kaduna sun gano gawar wata budurwa mai suna “Blessing John” a dakin wani otal dake Sabon Garin zariya, inda ciccire wasu sassa daga jikinta.
Bayanan da aka tattaro a kai shi ne, ana zargin ɗan dadiron ne ya halaka ta bayan kama dakin otal da suka yi tare domin goge raini.
An gano cewa, budurwar ta zo daga jihar Binuwai ne makonni uku da suka gabata inda ta tsunduma harkar neman kudi da jikinta a Sabon Garin zariya.
An tsinta gawar budurwanne wato “Blessing John” a dakin wani otal dake “Benin Street” a Sabon Gari dake Zaria ta jihar Kaduna.
Otal din da ya kasance tamkar gidan karuwai, an gano ana kai mata marasa daraja domin su fara Harkan dadiro.
Wani mutum dake zama kusa da otal din da ya bukaci a boye sunansa, yace, Ana zargin kwastoman budurwar ne ya halaka ta kwanaki biyu da suka gabata kafin a samu gawar wurin karfe 5:30 na yammacin Lahadi.
“Bayan shakar warin ne hankalin mutane ya kai dakin. An gayyaci ‘yan sanda kuma sun balle kofar tare da samun gawar. ‘Yan sanda sun dauka gawar tare da kai ta asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria.”
Daga bisani an sake ganowa cewa budurwar ‘yar asalin jihar Binuwai ce wacce ta iso Zaria makonni uku da suka gabata inda ta fada harkar neman kudi da jikinta kamar yadda muka ruwaito Hakan daga sama.
Jaridar ALFIJIR HAUSA ta tattaro cewa, an kama manajan otal din kuma ‘yan sanda sun garkame shi domin bincike.
Rahoto Zubair Ali Ibrahim.