An Tsíntà Jariri A Cikin Buhu A Anguwar Mu’azu Kaduna.
Mutane Sun Dimauta Bayan Da Aka Tsinci Jinjiri A Wani Kangon Da Ba A Karasa Ba A Kaduna.
MMutane sun dimauta bayan da aka tsinci jinjiri a wani kangon da ba a karasa ba a unguwar Mu’azu da ke cikin birnin Kaduna.
Mutane sun shiga damuwa bayan samun wani jariri kwance a cikin tsumma ba tare da kaya a jikinsa ba a unguwar Mu’azu da ke Kaduna babban birnin jihar.
Jaririn kamar yadda aka tabbatar an tsince shi ne a wani kango da ba a kammala ba a ranar Asabar 17 ga watan Yuni da misalin karfe takwas na safe.
Wani daga cikin ‘yan sa-kai da bai so a ambaci sunansa ba ya bayyana cewa jararin bisa dukkan alamu yana cikin koshin lafiya kuma ya ba da rahoton ga ‘yan sanda.
Mutane sun dimauta bayan da aka tsinci jinjiri a wani kangon da ba a karasa ba a unguwar Mu’azu da ke cikin birnin Kaduna.
Wani mutumin kirki ne ya tsinci jinjiri a ranar Asabar 17 ga watan Yuni tare da mika shi ga daya daga cikin ‘yan sakai a jihar da misalin karfe 8 na safe.
Daily Trust ta tattaro cewa jinjirin da aka tsinta yanasp cikin tsumma babu komai a jikinsa sai kunzugu, yayin da jinjirin ke cikin wani mummunar hali.
Daya daga cikin ‘yan sakai din da suka karbi jinjirin wanda ya bukaci a boye sunansa ya ce an samu jinjirin ne a kusa da wani kango kuma a cikin tsumma.
“Akwai alamun jinjirin na cikin koshin lafiya, kuma muna iya bakin kokarinmu don ganin mun kawo agaji.
“Sannan na kai rahoton wannan al’amari ofishin ‘yan sanda ta Kabala ta Yamma.”
A Kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar yaci tura saboda rashin samu lambar wayarsu.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim.