An yanke ma wasu ma’aurata a Iran hukuncin Shekaru 10 saboda rawa akan titi.
An yanke wa wasu ma’aurata ‘yan kasar Iran ‘yan shekara 20 hukuncin daurin shekaru 10 bayan sun yada hoton bidiyonsu na rawa a titi.
Rahotanni sun ce an same su da laifin yada rashawa, karuwanci da yada farfaganda.
Bidiyon ya nuna su na rawa da Hasumiyar Azadi (Freedom) ta Tehran.
Hukumomin kasar na zartar da hukunci mai tsanani ga mutanen da aka gani suna da hannu a zanga-zangar bayan mutuwar wata mata da jami’an ‘yan sanda masu da’a suka tsare.
Ma’auratan ba su danganta rawan da suke yi da zanga-zangar da ake yi a Iran ba.
Wata majiya ta tabbatar wa BBC Monitoring cewa kamen ma’auratan ya biyo bayan sanya faifan bidiyon a shafukansu na Instagram, wanda ke da mabiya kusan miliyan biyu.
Zanga-zangar adawa da gwamnati – wacce gwamnatin Iran ta yi wa lakabi da ” tarzoma – ta mamaye duk fadin kasar bayan Mahsa Amini mai shekaru 22 ya mutu a hannun ‘yan sanda a watan Satumbar bara. An kama ta ne a birnin Tehran bisa zargin karya dokar da ta ce mata su rufe gashin kansu da ‘hijabi’, ko kuma lullubi.
Astiazh Haqiqi, mai shekaru 21, da angonta Amir Mohammad Ahmadi, mai shekaru 22, an ce an same su da laifin “inganta cin hanci da rashawa da karuwanci, da hada baki a kan tsaron kasa, da kuma farfaganda kan kafa”.
Rahoto: Shamsu S Abbakar Mairiga.