An yi ga Gwamnatin Tarayya ta kir-kiri guraben aiki ga tsofaffi bayan ritaya.
Gwamnatin tarayya ya kamata ta kir- kiri guraben aiki bayan mutum yayi ritaya daga aiki, domin samun haduwar tsofaffun mutane, Wadanda ke fatan cigaba da aiki bayan sunyi ritaya.
Babbar darakta ta bai daya, Dr. Emem Omokaro na NSCC, tayi wannan bayanin A ranar laraba a yayin taron hadin gwiwa da wasu hukumomin gwamnati, Da kuma manyan ‘yan kasuwa masu rike da hannun jari a mataki babba a abuja.
Anyi ma taron take da “Cigaba da hadin gwiwar ayyuka, Kuma da burin gina wani kungiya tsakanin santar da kuma wasu membobi.
Omokaro tace, niyyar ya samo asali ne daga fahimtar irin muhimmancin da tsofaffin mutanen zasu iya bayarwa, wurin cigaban kasa.
Wani dalilin hadin gwiwar shine, domin ta taimaka ma santar ta hanyar kir- kirar guraben daukar ayyuka na kafafen sadarwa, Wanda hakan ne zai hada tsofaffin mutane, wadanda suke da kwarewa a maban bantan bangarori.
Wandan da hakan zai sa a hada mutane masu kwarewa, da basira ta cigaban al’umma.
Zamu kir-kiri platforms da shafuka, zamu kir- kiri gurabe ga tsofaffi wadanda suke fatan cigaba da bada gudunmawa, kuma suke da damar hakan, Saboda Kunsan mutane tsofaffi suna da damar bada gudunmawa a kowane sako duk a cewar ta.
Suna fatan hakan, kuma suna da damar yin kasuwanci bayan ritaya, ba wai dole sai gwamnati ta daukesu aiki ba.
Mun yadda cewa, tsofaffun mutane suna da rawar da zasu taka sosai domin cigaba Saboda suna da Skills, kwararri ne, dan haka zamu iya amfana daga wannan baiwar tasu, kamar yadda tace.
Mun kir-kiri portal saboda muna son duk wani bayani da muke son musamu, Ko kayi ritaya daga ma’aikatan gwamnatin tarayya ko jiha ko kananan hukumomi.
Mun kir- kirar wannan platform, sannan muma sanannun ne, muna so mu nuna kudin da najeriya take dasu, Kuma burin mu shine, NSCC ta kir- kiri dukiya, kamar yadda tace.
Babbar daraktan ta bai daya tace, portal din zai fara aiki a watan April.
Daga Rafi’atu Mustapha Katsina.