An Yi Garkuwa Da Malamin Jami’a Binuwai.
Wasu Barayi Sun Yi Awon Gaba da Malamin Majami’a a Jihar Benuwai.
Yan bindigan da ake zaton masu garkuwa da mutane don neman fansa ne sun yi awon gaba da Malamin Coci a jihar Benuwai
Wani ganau mai suna Oche, ya shaida cewa maharan sun shiga garin da karfe 10:00 na daren ranar Alhamis, suka wuce kai tsaye zuwa harabar Coci
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Benuwai, SP Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar lamarin
Wasu miyagun ‘yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa ne sun yi awon gaba da Malamin cocin Otukpo Diocese, Rabaran Anthony Adikwu.
Jaridar Punch ta tattaro cewa Malamin Cocin da maharan suka yi garkuwa da shi yana aiki a St. Margaret’s Parish da ke garin Ajegbe Awume, ƙaramar hukumar Ohimini a jihar Benuwai.
Wani ganau da ya bayyana sunansa da Oche a takaice, ya shaida wa wakilin jaridar cewa wasu ‘yan bindiga sun farmaki garin da misalin ƙarfe 10:00 na daren ranar Alhamis.
Ya ce daga zuwan yan ta’addan ba su tsaya wata-wata ba suka durfafi harabar Cocin, daga nan suka kwamushe Malamin suka tafi da shi maɓoyarsu da ba’a sani ba.
“A daren Alhamis da kusan karfe 10:00, wasu yan bindiga suka shiga garin Ajegbe Awume, karamar hukumar Ohimini ta jihar Benuwai. Kai tsaye suka zarce harabar Coci suka ɗauki Malamin da ke kula da majami’ar St. Margaret Parish.”
Yayin da aka tuntuɓe ta, Jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar yan sanda reshen jihar Benuwai da ke shiyyar Arewa ta Tsakiya, SP Catherine Anene, ta tabbatar da aukuwar lamarin.
“Rahoto ya iso gare mu da safiyar ranar Jumu’a kuma a halin yanzu muna kan aiki game da lamarin.”
Jihar Benuwai na ɗaya daga cikin jihohin Arewa ta Tsakiya da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga, waɗanda mafi akasari ake zaton makiyaya ne a sassan jihar.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim.