An yi jana’izar Fasto din da ya shekara 2 a mace don jiran farkawarsa daga matattu.
Iyali Sun Yi Jana’izar Fasto Bayan sun Jira Kusan Shekaru 2 Don Ya Tashi Daga Mutuwa Amma Laamri Ya Cutura.
An yi jana’izar wani babban malamin Addinin Kirista dan kasar Afirka ta Kudu, mai suna Siva Moodley, kwanaki 579 bayan rasuwarsa saboda iyalansa suna jiran tashinsa daga matatttu.
Jaridar ALFIJIR HAUSA ta ba da rahoton cewa; an ajiye gawar Moodley a dakin ajiyar gawa na Johannesburg tun mutuwarsa a ranar 15 ga Agusta, 2021.
Moodley mai shekaru 53 ya yi shelar cewa; zai iya ta da mutane daga matattu. Ya rasu ne bayan ya yi fama da rashin lafiya.
Rahotanni sun ce iyalansa da ’yan cocin sun kasance suna ziyartar gidan jana’izar don yi masa addu’ar Allah ya tashe shi daga matattu.
An ba da rahoton cewa manajan gidan jana’izar, Martin du Toit, ya shigar da bukatar Kotun Majistare ta Johannesburg don ba shi izinin a binne Moodley ko kuma a kona shi.