An Yi Yunkurin Halaka Dalibin Jami’a Akan Gardamar Kwallo A Bauchi.
Wasu Matasa Sun Lakadawa Dalibin Jami’a Duka A kan gardamar Kallon Kafa.
Wasu da ake zargin yan daba ne sun sari wani dalibin jami’a a jihar Bauchi bayan gardamar kwallon kafa ta barke a tsakaninsu.
Daya daga cikin yan daban ne dai ya sari dalibin mai suna Safiyanu Adamu da wukake har guda biyu a hannunsa.
Dalibin yana can kwance a asibiti ana duba lafiyarsa biyo bayan wannan aika-aika da aka tafka masa a kan kwallon kafa.
Yan daba sun sari wani dalibi mai suna Safiyanu Adamu, na jami’ar Sa’adu Zungur, da ke a Gadau a jihar Bauchi bayan barkewar gardamar kwallon kafa.
Jaridar Leadership ta kawo rahoto cewa, lamarin ya auku ne lokacin da ake wasan kwallo a tsakanin Green-White-Green House da GT House a ranar Asabar, inda daya daga cikin yan daban ya caka masa wuka.
Dan daban dai ya cakawa dalibin wuka ne a wuyan hannunsa na dama bayan gardamar ta rikide ta koma faɗa.
Safiyanu Adamu wanda yanzu haka ake duba lafiyarsa a babban asibitin tarayya da ke Azare, ya bayyana cewa ana cikin wasan wani da ake kira Lado yaje gida ya dauko wukake biyu wadanda ya sare shi da su a hannunsa.
Rahotanni sun nuna cewa daliban da suka yi ta maza suka tsaya da sauran wasu mutane sun ceto shi inda suka garzaya da shi babban asibitin Gadau, domin duba lafiyarsa.
An ba Safiyanu kulawar farko a babban asibitin na Gadau kafin daga bisani aka wuce da shi zuwa babban asibitin tarayya na Azare domin ba shi cikakkiyar kulawa.
Lokacin da aka nemi jin ta bakin kakakin rundunar yan sandan jihar, SP Ahmed Wakili, ya bayyana cewa zai tuntubi DPO din yankin kan lamarin kafin ya bayyanawa yan jarida halin da ake ciki.
Sai dai, wani dan sanda a Gadau ya bayyanawa yan jarida cewa suna bakin kokarinsu wajen yayyafawa lamarin ruwan sanyi kada ya rikide zuwa rikici bayan daliban sun fara shirin daukar fansa.
Ya ce kokarin na yan sanda ya haifar da ɗa mai ido domin zaman lafiya ya dawo a garin inda kowa ya ci gaba da gudanar da harkokinsa.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim.