An Zargi Basarake Da Laifin Yi Wa Yarinya Yar Shekara 5 A Gombe.
An Kama Wani Basarake Bisa Zargin Laifin Yiwa ‘Yar Shekara 5 Fyade A Karamar Hukumar Dukku.
A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne aka zargi basaraken da yi wa wata yarinya yar Shekara 5 cif fyaɗe a duniya.
Muh’d Yerima Muh’d hakimin lafiya tale a karamar hukumar Dukku dake jihar Gombe, shine wanda ya aikita wannan laifin sai dai zuwa yanzu dai an ƙwace rawanin basaraken bayan da kama shi da zargin laifin aikata fyade dumu-dumu.
Sai dai a wata majiyar ma zauna garin su bayyana cewa, wannan ba shine karo na farko ba daya yake aikata irin wannan aika-aikan.
Haka zalika iyayen yarinyar sun bukaci mahukunta dasu bi musu kadu bisa irin cin zarafin da ya yiwa ‘yar su mai shekaru biyar da haihuwa.