Daga Hajiya Mariya Azare.
Ana zargin wasu dattijai guda uku da yima wata wata matashiyan yarinya ‘yar shekara sha uku fyaɗe a wani gidan biredi, dake tudun wada zariya Jihar Kaduna.”
Wata majiya tace dattijan dai sun ɗauki lokaci suna yima yarinyan fyaɗe, harsai da mahaifiyanta tafara ganin wasu alamu na canji a tattare da ita, mai unguwan gangaren kwaɗi Malam Mohammad Danliti, ya tabbatarwa jaridan Aminiya faruwan lamarin inda yace bayan da mahaifiyanta ta gano wasu alamun canji a jikinta batayi tunanin cewa wasu ne suka aikata mata hakan ba.”
Yace, sai daga baya ɗaya daga cikin ƙawayen kurma ta sanar da mahaifiyanta cewa tana ganin bebiyan tana yawan zuwa gidan biredin ana bata kuɗi.
Jaridan Aminiya tayi bincike zuwa asibitin Gambo sawaba, inda aka kai yarinyan domin duba lafiyanta wanda likitoci suka tabbara da anyiwa yarinyan fyade kuma harsun saka mata cuta.”