An zargi Hukumar NDLEA da Bindige wani Matashi har lahira a Garin Zariya.
A ranar juma’a ne 27 da misalin karfe goma sha biyu na rana jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA reshen Zariya, suka yi Dirar mikiya a dakin wani matashi me suna Sani (Aci) dake gidansu a tudun wada zari’a. In da bayan yunkurin kama shi da bai ci Nasara ba suka harbeshi a kafa da kwibin cikinsa na gefen hagu da yayi sanadin Mutuwarsa bayan kai shi Asibitin Shika Zariya.
Wakilin Jaridar ALFIJIR HAUSA wanda ya ziyarci anguwar da abun ya faru kuma ya bi diddigin lamarin tare da zantawa da wadanda abun ya faru akan idonsu, an tabbatar masa da cewa Jami’an hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyin sun shiga har dakin matashin a yunkurinsu na tasa keyarshi zuwa ma’aikatarsu, al’amarin da ya gamu da turjiya daga Matashin Sani Aci kamar yanda ganau suka shaidawa wakilinmu.
Har ila yau ganau din sun kara da cewa matashin Sani Aci ya cire wuqa a lokacin da suka yi koqarin tafiya da shi ya yanki wasu daga cikin Jami’an hukumar NDLEA din,daga nan matashin ya kama katanga don haurawa a yunkurinsa na guduwa, Al’amarin da ya gamu da cikas sakamkon daya daga cikin ma’aikatan NDLEA da take ya harbeshi a gefen cikinshi da kuma kafa, wanda ya ba su damar kama shi tare da daukarsa zuwa Asibiti inda aka tabbatar musu da rai yayi halinsa.
Daga baya yan uwan mamacin suka je suka karbo gawarsa, kuma tuni aka gudanar da jana’izarsa a kashegarin Asabar a layin imamu dake tudun wada zari’a.