An zargi yan Sanda da Bindige wani mutum kan cin hanci na 100 a Delta.
Matasan jihar Delta sun afkawa hedikwatar ‘yan sanda da gawar wani mutum da ake zargin yan Sandan sun kashe shi Saboda 100.
Wasu fusatattun matasa a jihar Delta a ranar Laraba, 5 ga watan Afrilu, sun kai farmaki hedikwatar rundunar ‘yan sandan jihar tare da gawar wani matashi da ake zargin wasu jami’an ‘yan sanda sun bindige shi kan ‘’ cin hancin N100’ a kan hanyar Ugbolu zuwa Asara.
Matasan sun tare wata babbar hanya a garin Asaba domin nuna rashin amincewarsu da Abinda yan Sandar Sukayi.
Har yanzu dai rundunar ‘yan sandan jihar ba ta ce uffan ba kan wannan lamari.