An zargin makiyaya da sun kashe shugaban sanda, DPO da wasu mutane biyar a Benue.
Abubakar wanda shi ne jami’in ‘yan sanda shiyya ta Naka reshen karamar hukumar Gwer ta yamma, an yi zargin an yi masa kwanton bauna ne a ranar Talata da misalin karfe 3:30 na rana.
Wasu ‘yan bindiga sun bayyana cewa sun kashe wani Sufeto na ‘yan sanda na rundunar ‘yan sandan jihar Benue, Mamud Abubakar.
Abubakar wanda shi ne jami’in ‘yan sanda shiyya ta Naka reshen karamar hukumar Gwer ta yamma, an yi zargin an yi masa kwanton bauna ne a ranar Talata da misalin karfe 3:30 na rana.
Rahotanni sun ce an kashe DPO din ne a lokacin da yake dawowa daga Makurdi, inda ya je yi masa rakiya.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Wale Abass, wanda ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a ranar Talata, ya ce an fara farautar maharan.
Ya ce, “Gaskiya ne an kashe DPO; yaje rakiya ne suka share masa hanya. Akan hanyarsa ta zuwa Naka suka yi masa kwanton bauna.”
An kuma bayar da rahoton cewa, ‘yan bindigar sun kashe mutane biyar a tsakanin ranakun Lahadi zuwa Talata, ta hanyar wasu ‘yan bindiga da ake zargin makiyaya ne a wasu al’ummar karamar hukumar, kamar yadda rahoton PUNCH ya ruwaito.
Shugaban karamar hukumar Gwer West, Ayande Andrew, ya yi ikirarin cewa makiyaya ne suka kashe DPO din.
Ya ce, “Makiyaya ne suka tare hanyar kuma DPO na kan hanyarsa ta zuwa Makurdi ne suka yi masa kwanton bauna; shi kadai ne a cikin motar da ke kan hanyar.”
A kan sauran biyar da aka kashe, ya ce, “Makiyaya sun kashe wani a safiyar yau (Talata) a kauyen Tsenge, sannan kuma an kashe wasu mutane hudu a unguwar Babowa ranar Lahadi.”
Daga Rufa’i Abdurrazak Bello Rogo.