Ana zargin IPOB da kona babban kotu tare da kashe babban Alkali a Imo.
Wasu ‘yan bindiga da ake zargin yan IPOB ne a daren Lahadi sun kona babbar kotun Oguta da ke karamar hukumar Oguta a jihar Imo.
An tattaro cewa maharan sun isa ne da misalin karfe 11:30 na dare inda suka kai hari a cibiyar da ke cikin hedikwatar karamar hukumar.
Wata majiya, wacce ba ta son a ambaci sunansa saboda dalilai na tsaro, ta shaida wa jaridar Alfijir hausa news LTD cewa, rajistar Kotun Majistare, Ofishin Rakodin Kotun Daukaka Kara, Dakin Fayil, Sakatariyar Ofishin Alkalin Babbar Kotun, ofishin Babban Kotu, an kona zauren alkalin babbar kotun.
Majiyar ta ce, “An kona rajistar Kotun Majistare, Ofishin Rakodin Kotun Daukaka Kara, Dakin Fayil, Ofishin Alkalin Kotun, da ofishin Babban Kotun Koli, yayin da aka kona wani bangare na Alkalin Kotun.
Gaba dayan katangar ya fashe kuma babu wani mahaluki mai hankali da zai taba zuwa kusa da wurin.”
Rundunar ‘yan sandan jihar Imo ta cafke wadanda ake zargin IPOB ne suka kai harin.
Shugaban karamar hukumar Oguta, Ofili Ijioma, ya ce an kai rahoton faruwar lamarin ga jami’an tsaro.
Ya kuma tabbatar wa da wakilinmu cewa bincike zai bankado fuskokin maharan nan kurkusa.
Harin na baya-bayan nan ya zo ne kwanaki 10 bayan kashe alkalin da ke kula da kotun al’adun gargajiya ta Ejemekwuru, Nnaemeka Ugboma, a lokacin da yake jagorantar zaman kotun.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Henry Okoye, ya ce har yanzu yana jiran bayanai daga yankin.
Daga Salmah Ibrahim Dan mu’azu.