Ana zargin kawo cikas a zaman kotu gobe da za’a yi kan kasuwar yan lemo Maraba.
Ana zargin kawo cìkàs a zaman Kotun gobe da za’a gabatar akan kasuwar ƴan lemo dake garin mararaban gurku a jihar Nasarawa,
Jaridar Eyeshadow ta rawaito cewa, wani màkusancin kàsuwar ya jiyo wata shiri da wasu ke shiryawa na kawo cìkàs a zaman Kotun da za’a gabatar a gobe litinin, inda ya bukaci a ɓoye sunansa saboda rashin tsaro.
Idan baku manta ba, makonni biyu da su gabata ne fitaccen ɗan jarida kuma dan kasuwa a garin maraba Alhaji Sani Ahmad zangina ya shigar da karar kasuwan inda ya bukaci kotu ta karɓa masa kasuwansa a hannun jagororin kasuwan.
Inda kotu ta sanya ranar 15 ga watan Mayun 2023 a matsayin ranar zama na gaba.
Sai dai bayan fitowar labarin shirin tayar da rikicin ya sanya hankular Alumma da dama suna kiranye-kiranye da a dauki mataki kawo jami’ai kafin zaman na gobe.