Ana zargin wata Mata da Kashe Kanta saboda Za’ai mata kishiya a Zaɓin Zariya.
A Larabar da ta gabata wani Abun al’ajabi wanda ya bawa mutane mamaki ya faru a wani gari da ake kira da zaɓi na Sabon garin zariya lamarin da mutane sun ce su sai a shirin Fim na Indiya suka saba gani.
Lamarin da ya sanya mutane cikin kokonto da jinjina abin domin bai taɓa faruwa a yankin ba sai wannan lokacin hakan ya sa wasu suke cewa anya wannan abun kuwa ya faru.
Wata mata a cikin garin Zaɓi ƙaramar hukumar sabon garin zariya ta rataye kanta saboda mijinta zai ƙara mata abokiyar zama hakan ya sanya zuciyarta ya kaɗu ta kashe kanta
Jaridar ALFIJIR HAUSA ta binciki labarin tiryan tiryan domin ji da ganiwa ido lamarin da kuma jin abubuwan da al’umma ke faɗa a kan lamarin kisan kan.
A yanda labari ya same mu shi ne mutan gidan da suke tare da matar sun labarta mana cewa matar ta je mahaifarsu domin gaida iyayenta bayan ta dawo gida.
Sai mijinta ya ɗauke ta ya kaita sabon giɗan da ya gina musu har ya na mata wasa da cewa wannan shine ɗakin ki wannan kuma na amarya.
Hakan ya sanya zuciyarta hasala amma bata nuna masa cewa taji zafi ba sai bayan dawowarsu gida ta zauna tare da mutan gida ana fira sai kawai ta tashi ta shiga ɗaki ta haɗa abubuwan da zata kashe kan nata.
Bayan ta kammala komai na haɗa kayan rataye kan nata sai ta sanya Turmi a wajan ta hau tare da yaron ta tagoyasa a bayan ta cikin wasu ƴan lokuta mutanan gida sai suka jiyo kukan yaro da mutsu mutsu na da kakarin mutuwa.
Mutan gidan basu yi ƙasa a gwiwa ba suka habzarta cikin ƙakkanin lokaci suka shiga ko da shigarsu matar ta mutu yaron da ke bayan ta sai ihu ya keyi.
Hakan ya sa akayi ihun kiran Ceton rai ko da zuwan jami’an tsaron da ke kula da turawan da ke aikin hanya gida ya cika da mutane ganin yawan mutane yasa jami’an tsaron suka tabbaya mai ke faru.
Bayan angaya musu suka shiga cikin gidan suka ƙira jami’an hulɗa da mutane wato ƴan sanda suka kwance ta suka tasa ƙeyar mijinta tare da ƙaninsa domin bincikarsu.
Sai dai mutane da dama sun ce ita wannan wacce ta kashe kan nata ƴar asalin jihar Katsina ce ba a jima da auro ta ba domin ko shekara biyu ba tai ba a gidan mijin nata.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim Gwado.