Anlika takardar Kotu gidan sabon gwamnan Kebbi abisa kin amsa sammacin kotu
Rahoto:- Comrade Yusha’u Garba Shanga.
“Kamar yadda kowa yasani abisa zaben Gwmanoni a Najeriya zango na biyu, jihar Kebbi da Adamawa sune wadanda rukunin zaben nasu yazo da wasu kalubale tareda rashin kammala zaben ba abisa yadda hukumar zaben kasa ta tana dar ba.
“Hakan ya janyo dage zaben har wani karo da suna “(Inconclusive)” a cewar dokan zabe. “Bayan Share daukar wasu makonni, ansake gudanar da zaben sama da rumfa 143 a faɗin Jihar, wanda yazam an bayyana dan takarar jam’iyyar APC amatsayin mai nasara.
Biyo bayan hakan, jam’iyyar adawa ta PDP tayi watsi da rashin amincewar ta ga wannan hukunci da INEC ta sanar a matsayin sonkai dakuma ra’ayi wanda hakan ya haifar da shigar da kararsu a “(TRIBUNAL COURT)” dake jihar.
“Jam’iyyar PDP da Ɗan takarar ta Gen. Aminu Bande Rtd sun bayyana zaben da ya gabata na gwamnoni musamman jihar Kebbi amatsayin cin amana da zagon kasa wanda jam’iyyar APC tayi abisa hana wasu kauyuka fitowa zaɓe, siyen ka tunan zabe, Aringizo, ciki harda tsofaffin takardun zabe na shekarar 2019 dakuma almundahara.
Kamar yadda wakilin Alfijir Hausa ya tattaro mana bayanai, Comrd Yusha’u Garba Shanga yace:-
Acikin wata fira da shugaban kwamitin yada labarai yayi na jam’iyyar PDP, (Alhaji Sani Dododo) a tashar Equity FM dake birnin Kebbi yace., Sama da kwana ashirin da daya da tura Sammacin Kotu ga jam’iyyar dakuma dan takarar sunki amsawa bale ko inkuka.
“Kotu ta bada Umurni, an liƙa Sammaci da aka aika ga ɗan takarar Gwamnan APC na Jahar Kebbi Wato “Nasir Idris(Ƙauran-Gwandu) da mataimakinsa “Sen.Umar Abubakar Argungu”(Tafidan-Kabi) wanda anka aika musu sunka ƙi karɓa.
An liƙa wannan sammaci ne a Ofishin jam’iyyar APC na Jahar Kebbi, gidan dan takarar da mataimaki sa da kuma saman Allo na bakin kofar shiga kotun sauraren kararrakin zaɓe(TRIBUNAL) abisa ga Umurnin Kotu.
Yace har yanzu da sauran lokaci da ya rage ga jam’iyyar wanda kotu ta bayar da damar zama, idan lokacin yayi basu halarta ba hurumine na kotu data zartar da hukuncin ta na gaskiya abisa yadda doka ta tanadas.