Anyi garkuwa da wata mata bayan ta bayyana zatayi tafiya a shafinta na fesbuk a katsina.
Wata mata mai suna Ramlat Alhaji Shehu, anyi garkuwa da ita a hanyanta na zuwa katsina daga kagara a karaman hukuman Rafi ta jahan Naija.
bayan ta bayyana inda take a fasbuk.
Ramlat ta bayyana a shafinta na fesbuk cewan,tana kan hayanrta na zuwa funtuwa amma bata isa inda zata nufa ba.
Tunda ta bayyana tana kan hanya ‘yan uwanta sukaji, inda haryanzu haka annemeta anrasa.
Daga baya aka samu labarin cewa, tana hanun ‘yan bindiga inda suka nemi kudade masu yawan gaske a hannun ‘yan uwanta.
Wani wanda abin ya shafa mai suna Alhaji Abdullahi Dan gaske ya bayyana cewa, yanzu tilas ne mutane su kula wajen wallafa inda suke a kafafen sada zumunta.
Yace, masu garkuwa da mutane sun yadu a ko’ina a shafukan sada zumunta kuma suna ganin dukkan abubuwan da kowa yakeyi inji shi.
Rahoto Hajiya Mariya Azare.