Wani mutum a jihar Adamawa ya gurfana a gaban kotu da laifin sanya tufafin mata domin ya yaudarari samari ta hanyar ya ci kuɗin su.
Mutumin mai suna Muhammed Abubakar ya ce ya kan sanya kayan mata ne da kuma fita da abokansa mata domin samun kuɗi a wajen maza masu buƙatar soyayya.
Muhammed wanda ke da Diploma a fannin kasuwanci daga Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Adamawa, Yola, ya ce matan da suke yin irin wannan aikin tare suna ba shi tsakanin Naira 500 zuwa N1,500 a kullum a matsayin kason shi.
Muhammed, wanda ya ce yana amsa sunan mace inda ya shaidawa babbar kotun majistare da ke Girei inda aka gurfanar da shi a gaban kotu, cewa masu laifin mata na kare shi a duk lokacin da wani mutum ya buƙaci ya bashi haɗin kai, sai sauran matan su gaya wa mutumin cewa ita (shi) tana cikin haila ne.
Manema labari sun tabbatar da cewa a jiya ne wasan Muhammed ya ƙare ne a kasuwar Girei inda ya je sayan zoben kunne sai wani mutum ya gan shi wanda ya yi zargin cewa shi namiji ne. Kotun ƙarƙashin jagorancin Martina Gregory ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare shi har zuwa ranar 5 ga watan Disamba.
Daga Aliyu Adamu Tsiga.