“A yau Asabar ne jagororin sauran jiga-jigan jam’iyyar PDP suka halarci wajen ƙaddamar da Cibiyar Dimokraɗiyyar Jama’a, wanda Ɗan takaran shugaban kasar Nijeriya Alh. Atiku Abubakar ya ƙaddamar.”
Rahoton na cigaba da cewa, Cigaba ne da al’ummar Nijeriya za su yi alfahari da shi, musamman. Cibiyar za ta taka muhimmiyar rawa wajen ganin an dawo da martabar dimokuraɗiyya a ƙasarmu da ma nahiyoyin duniya.”
“Taron ya samu haɗin kan jiga-jigan jam’iyyar na PDP, inda aka samu jawabai masu muhimmanci ga su mahalarta taron.”
Bayan haka kuma Ɗan takaran shugaban kasar ya cigaba da jawabai masu ratsa jiki na ire-iren alƙawuran da ya yi wa Ƴan Nijeriya.”
“Atiku Abubakar ya tabbatar cewa, zai taka muhimmiyar rawar gani domin ganin farfaɗo da tattalin arziƙin Nijeriya, tare da manyan ƙudurorinsa na Alkhairi.”
“Har Wala yau dai a cikin jawaban na Ɗan takaran shugaban kasar, inda ya sha alwashin samar da kafofin dogaro da kai, tare sauƙaƙa dukkan ababen more rayuwa ga al’umma.”