Manufar da Ƴan Nijeriya suka daɗe suna dako Atiku ya yi alƙawarin farfaɗo da su.”
“Mai Girma Tsohon mataimakin shugaban kasar Nijeriya, kuma Ɗan takarar Shugaban Kasa a Karkashin Jam’iyyar PDP a zaben 2023, Alhaji Atiku Abubakar Wazirin Adamawa, yayi alwashin Ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman, mai inganci, mai sauki kuma mai ɗorewa na bunƙasa harkokin kasuwancin ƙasa da samar da ayyukan yi ga al’ummah, wanda zai matukar taimkawa wajen cigaban ƙasa.”
Ɗan takaran shugaban ƙasar ya ce Babban manufarsa shine ganin Nijeriya ta dai-daitu, musamman daga faɗawa mummunar talauci da aka ƙaƙaba mata da ƙarfi.”
“A cigaba da bayyana manufofinsa na Alheri, Atiku Abubakar ya cigaba da nuna alhininsa Dangane da yadda makomar Nijeriya takasance aciki a halin yanzu, na rashin tsaro.
Ɗan takarar shugaban ƙasar ya tabbatar da hakan lallai Ƴan Nijeriya za su samu kwanciyar hankali, walwala, sauƙin rayuwa, wadatuwan aikin yi, da sauran makamantansu.”
Atiku Abubakar ya cigaba da bayyana manufofinsa inda ya ka da baki yake cewa suna da manufofi ƙwarai akan Ƴan Nijeriya tare da tabbatar da ganin gwamantinsa ta yi adalci.