Atiku Da Ayu Sun Ziyarci Waɗanda Haɗarin Yakin Neman Zaben PDP Ya Shafa A Filato
Dantakarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya ziyarci wadanda hatsarin mota ya rutsa da magoya bayan jam’iyyar da suka dawo daga karamar hukumar Mangu wajen yakin neman zaben shiyyar Tsakiyar Jihar Filato a Pankshin ranar Asabar.
Ya ziyarci shugaban jam’iyyar na kasa Sanata Iyorchia Ayu inda ya bayar da tallafin Naira miliyan 30m ga wadanda abin ya shafa.
Hatsarin ya afku ne a kusa da kauyen Jwak dake gundumar Panyam a karamar hukumar Mangu a jihar Filato inda aka tabbatar da mutuwar mutane 16 tare da jikkata wasu da dama.
Atiku, Ayu da wasu fitattun mutane ne aka kaisu sashin bada agajin gaggawa na asibitin koyarwa na jami’ar Jos (JUTH) da dan takarar gwamnan Filato na jam’iyyar Barista Caleb Mutfwang (BCM), inda suka gana da wadanda abin ya shafa don jajanta musu da kuma yi musu addu’ar samun lafiya.
Atiku da tawagarsa sun kasance a gidan tsohon gwamnan jihar, Sanata Jonah David Jang, domin jajanta masa kan lamarin.
Haka kuma mai fatan zama shugaban kasar ya ziyarci Mishkaham Mwaghavul, da mai martaba Daa John Putmang Hirse, wanda ke tare da shugaban su na kasa, Mwaghavul Development Association (MDA), Sir Joseph Gwankat, da wasu mambobin majalisar gargajiya na Mwaghavul.
Ya jajantawa al’ummar Mwaghavul tare da addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu a hatsarin.
Mishkaham Mwaghavul ya karbi ta’aziyyar Atiku Abubakar a madadin al’ummar karamar hukumar Mangu.
Dan takarar shugaban kasa ya bayar da gudummawar Naira miliyan 30 ga wadanda hatsarin ya rutsa da su yayin da Ayu ya bayar da Naira miliyan 10 a madadin jam’iyyar, wanda ya kai adadin zuwa Naira miliyan 40.
An sallami mutane da dama da suka tsira da suka rage a asibitin Nisi Dominus, biyu kuma a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Bethel ta Nanret, duk a karamar hukumar Mangu.
Daga cikin mutane 28 da aka kwantar a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos JUTH, uku an sallame su.