Ɗan takaran tare da tawagarsa, sun gana da ƙungiyar Editocin Najeriya a safiyar yau Laraba.”
“Wannan wata dama ce da shi ɗan takaran ya bayyana na shirinsa na Mai da Najeriya da su. Zaman tattaunawa ne.”
Kuma Ɗan takaran ya yi matuƙar godiya da irin karimcin da editoci suka yi wajen gayyatarmu.”
Atiku Abubakar ya nuna farin cikinsa kan wannan zama da suka gudanar tare nuna su mahalarta wannan taro godiyarsa, musamman da irin karramawar da sukai masa.”
Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa zai mayar da Najeriya cibiyar tace danyen mai a nahiyar Afirka ta hanyar mayar da matatun mai zuwa wani kamfani.
Ɗan takaran yace matatun man fetur na Nijeriya zai sauya mata fasali zuwa wani kamfani da kuma mayar da Najeriya cibiyar tace danyen mai a Afirka.” Atiku ya wallafa a shafinsa na Tuwitta.
Ɗan-takaran ya tabbatar da waɗannan kyawawan manufofin masa idan har ya ci babban zaɓe na kakan bana na shugaban kasa dake tunkaro mu.”
Atiku Abubakar ya cigaba da bayyana kyawawan manufofinsa kan makomar Nijeriya dazaran ya zama shugaban ƙasa a nan gaba, ya ƙara bayyana cewa burinsa shine matasa su samu aikin yi musamman ƳaƳan talakawa.”
Ɗangane da Harkan tsaro Ɗan-takaran shugaban kasar yace gwamantinsu zata yi ƙoƙarin ganin ta kawo ƙarshen ta’addanci Nijeriya, tare da ƙarawa fannin tsaro ƙarfi matuka.”
Ɗan takaran ya kuma ce Dangane da abinda ya shafi tsadar kayan masarufi tabbas ya yi aniyar gwamantimsa zata sauƙaƙa manufar tashin Gwauron zabin da kayayyakin ke yi.”