Ɗan takaran Shugaban ƙasa tare da mataimakinsa Ifeanyi Okowa, a halin yanzu sun tattauna ta kasuwanci tare da shugabanni da mambobin kamfanoni masu zaman kansu na Najeriya a birnin Legas.
Zaman yana da manufar yadda za’a raba shirye-shirye na farfaɗo da Nijeriya daga mummunar yanayin da take ciki.
Ɗan takaran shugaban kasar ya nuna farin cikinsa ganin yadda shuwagabannin kamfanonin suka bashi haɗin kai domin tattaunawa da juna don ƙara samun fahimtar juna, musamman kan yadda za’a farfaɗo da tattalin arziƙin Nijeriya idan ya samu ragamar kasar a hannunsa.
Zaman ya samu mahalarta daban-daban magoya bayan Ɗan takaran Shugaban ƙasa, inda suma suka yaba da irin manufofin ɗan takarar shugaban ƙasar.”
Atiku Abubakar ya bayyana cewa, tabbass Nijeriya tana buƙatar agajin gaggawa domin farfaɗo ƙasar daga hannun Ƴan handama da babakere, duba ga yadda aka jefa ƙasar a cikin taluaci da halin ƙaƙayi ƙani.