Atiku zai gabatar wa da kotu asalin sakamakon zabe da ke nuna shi ya yi Nasara.
Wani dan jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), Emma ik Umeh, ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, Atiku Abubakar, zai gabatar da dukkan takardun sakamakon farko a kotun daukaka kara.
A cewar Umeh, wasu daga cikin takardun da ya gani suna tayar da hankali, inda ya kara da cewa ba zai iya jira a fara shari’ar kotun zabe ba.
Takardun da PDP da Atiku suke gabatarwa kotun daukaka kara, a cewar Umeh, ba wasan yara bane. Ya bayyana hakan ne a shafin sa na Twitter.
“Takardar da PDP da Atiku suke gabatarwa a kotun daukaka kara ba wasan yara bane. Suna da duk takaddun sakamako na asali. Wasu takardun da na gani suna da ban tsoro. Ba zan iya jira a fara shari’ar kotun zabe ba.”