B0k0 Haram Sun Bayyana Mani Dalilinsu Na Daukan Makami – Obasanjo
Daga Al-Asad Al-Amin Funtua
Cif Olusegun Obasanjo, tsohon shugaban ‘kasar Najeriya, a ranar Juma’a, ya yi ikirarin cewa wadanda suka kafa kungiyar B0k0 Har*m sun shaida masa cewa talauci da rashin aikin yi ne suka zaburar da su aikata laifuka a farkon rikicin a Arewa-maso-Gabas.
Sai dai ya yi gargadin cewa idan ba a gaggauta magance yara kusan miliyan 20 da ba sa makaranta, to za su zama wata matattarar ‘yan B0k0 Har*m nan gaba.
Tsohon Shugaban kasar ya bayyana haka ne a ranar Juma’a a wajen kaddamar da wani littafi mai suna, ‘Pillars of Statecraft: Nation-building in a Change world’ wanda ‘yarsa, Dokta Kofo Obasanjo-Blackshire ta rubuta a wani taron da aka yi a Legas.
Da yake mayar da martani ga wata tambaya da wani dan kallo ya yi masa kan dalilin da ya sa matakan gwamnati na baya-bayan nan suka zama siyasa fiye da na jama’a, ya bayyana cewa daya daga cikin batutuwan da al’ummar kasar ke ci gaba da fuskanta shi ne na neman tsira daga matsalolin da suke fuskanta.
Ya ci gaba da cewa, “A farkon shekarun B0k0 Har*m, da aka ce an kashe mutumin da ya ‘kirkiro kungiyar, sai na ce ina so in gana da ‘ya’yan kungiyar domin mu tattauna da su, na san abin da suke so, na gana da wakilansu na gano cewa ba su bukatar komai sai rayuwa mai inganci.
Sun ce suna bukatar Shari’a, na ce musu Sharia ba matsala ba ce a Najeriya, yana daga cikin kundin tsarin mulkin mu.
A cewar tsohon shugaban, wasu daga cikin ‘ya’yan kungiyar masu tayar da kayar baya sun shaida masa cewa sun je makaranta amma ba su da aikin yi.
Sai dai ya yi gargadin cewa idan ba a bullo da wata hanya da zata gaggauta magance yara kusan miliyan 20 da ba sa zuwa makaranta, to za su zama wata matattarar ‘yan B0k0 Har*m nan gaba.
Wadancan su ne tushen B0k0 Har*m, ya kamata mu damu, kada mu ce an jawo shi daga waje. Talauci kuma daga waje ake jawo shi? Talauci zabin shuwagabannin mu ne, Idan muka ce a’a; ba zai kasance ba. Idan muka ce eh; zai zama eh,” inji Obasanjo.
A watan Yulin shekarar 2009 ne rikicin B0k0 Har*m ya fara a jahar Bauchi ya kuma bazu zuwa wasu jahohin Arewacin ‘kasar, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mabiya kungiyar da jami’an tsaron Najeriya da kuma fararen hula.
A shekara guda bayan rikicin kungiyar, aka fara kai hare-hare a Arewa maso Gabas da sauran sassan ‘kasar nan da suka hada da tashin bama-bamai da harbe-harbe da kisa.