Ba a ba ni izinin shiga Dubai ba saboda kyamarar Fasfo bai yarda da fuska na ba” – Bobrisky.
Shahararren mai kamaiceceniya da mata wato Bobrisky da yake magana a faifan bidiyo, ya ce: “Lokacin da ya je Dubai, an dawo da shi Najeriya, Ya kara bayyana cewa; ya sha zuwa wurin yin fasfo sau da yawa. kyamarar ba ta karɓi fuskarsa ba.
Bobrisky ya ci gaba da cewa; An san shi, kan kayan shafe-shafe ana kuma kyautata zaton yawan shafe-shafenne yasa kyamarar bai hau fuskarsa ba.”
Don haka, bayan ya ga Lamarin ya cutura sai ya garzaya wurin hukumar masu kula da shige da fice wato “Immigration” inda yake tunanin komai zai dai-daita masa domin kamun kafa a nanma Lamarin ya cutura.
Ya dai ci gaba da kara fashin baki kan cewa; har Yanzu dai yana ci gaba da fafautuka har sai wannan kyamarar na Fasfo ya dauki fuskarsa, domin yana son Rayuwar kasar Dubai zuwa ya gagaresa.