Ba dagangan bane jinkirin Shari’ar Alhassan Doguwa kan zargin kisa.
Gwamnatin Jihar kano ta mayar da martani akan zargin da wasu ‘yan fafutuka keyi cewa, Taki gurfanar da shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai agaban kotu.
‘Yan sanda sun kama Alhassan Ado Doguwa a karshen watan Fabarairu, Inda suka kai shi kotun majistare bosa zargin ya harbi wasu mutane, kwana daya bayan zaben shugaban kasa A mazabar sa ta Doguwa/Tudun wada.
Sun kuma tuhumi dan majalisar wakilan da kashe mutum uku, da raunata wasu takwas A karamar hukumar Doguwa lokacin da ake karbar sakamakon zabe.
Kotun dai ta ba da umarnin a cigaba da tsare wadanda ake zargin a gidan yari, kafin fara shari’ar gadan gadan, Amma an ga shugaban masu rinjayen a cikin wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, Kafin ‘yan sanda su kama shi, yana musanta zarge- zargen haddasa tashin hankali a lokacin zaben.
Sai dai, kwana daya kafin a mayar da shi kotun majistare, sai wata babbar kotun tarayya a kano ta bayar da belin dan siyasar ranar 6 ga watan maris, Tun daga lokacin kuma ba a sake jin batun komawa don cigaba da shari’ar ba.
Lamarin dai ya sa bangarori da dama sun fara zargin ko hukumomi a kano, Na kokarin danne maganar, har ta bi ruwa.
To amma a martanin da ta mayar ranar laraba, ma’aikatar shari’ar jihar kano tace, ba da gangan, taki kaishi kotu ba.
A cewar ta, jinkirin da aka samu wajen ci gaba da shari’ar, wani al’amari ne, ma kokarin bin tsari don tabbatar da adalci ga kowanne bangare.
Kwamishinan shari’a na jihar Kano, Musa Abdullahi Lawan yace, tun lokacin da aka fara gabatar musu batun Alhassan Ado Doguwa, Suka lura cewa, akwai Kura- Kurai.
“Don kuwa akwai wasu batutuwa da ba a shigar da su cikin takardun da suka shafi zarge- zargen da ake yi wa dan siyasar ba, inji shi.
Daga Rafi’atu Mustapha Katsina