Ba Zan Bar ‘Yan Najeriya Su Yi Asarar Tsoffin Kudi Ba Idan Suka Zabe Ni Shugaban Kasa –Atiku
Dantakarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar, ya soki tsarin babban bankin Najeriya CBN na canjin fasalin kudi a kasar.
Atiku ya bayyana hakan ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.
“Manufar CBN kan kudi tana jefa talakawa marasa karfi da wadanda suka tara kudaden su ta halartacciyar hanya cikin mawuyacin hali.”
“Dole ne babban Bankin na ƙasa ya gaggauta bada dama ga bankunan kasuwanci su shiga aikin karɓar tsofaffin kuɗi na N500 da N1000.”
Wajibi ne a samar da sababbin takardun kuɗin cikin hanzari kuma wadatattu domin rage raɗaɗin wannan tsari ga talakawa.”
Ina baku tabbacin cewar idan muka hau mulki bayan kun zabe mu gwamnatin PDP ba zata bari wani ɗan Nijeriya ya yi asarar sisin kwabo da ya tara ta halartacciyar hanya ba, zaku iya kai kuɗin ku banki, saboda manufar mu ita ce samar da walwala ga ƴan Nijeriya ba mu jefa su cikin mawuyacin hali ba.” Inji Atiku.