Ba zan fasa korar Ma’aikata da rusau ba har karshen Mulki Na, Gwamna El Rufa’i.
Gwamnan jihar Kaduna ya sha wani muhimmin alwashi yayin da ya ke tunkarar karewar wa’adin mulkinsa a ranar Litinin 29 ga watan Mayu
Nasir El-Rufai ya sha alwashin kakkaɓe duk wasu baragurbi a gwamnatinsa har zuwa ranar da zai yi bankwana da mulki
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen ƙaddamar da wani littafi a birnin Kaduna ranar Asabar, 20 ga watan Mayu
Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, ya sha alwashin ci gaba da korar duk wani baragurbin ma’aikaci da ya cancanci a kore shi a gwamnatinsa, da rushe duk wani gini da ya cancanci rusau har zuwa lokacin da wa’adin mulkinsa zai kare.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 20 ga watan Mayun 2023, a wajen bikin kaddamar da wani littafi wanda ya yi magana a kansa, rahoton The Nation ya tabbatar.
Littafin wanda fitaccen ɗan jarida Mr Emmanuel Ado, ya wallafa, an sanya masa sunan “Putting The People First,” cewar rahoton Daily Trust.
El-Rufai ya ce zai ci gaba da rusau ne domin kawo gyara ta yadda magajinsa, idan ya zo ba sai ya sake yi ba.
“Duk wani abinda mu ka ga bai dace ba, za mu cire shi ta yadda gwamnan da zai zo bayan mu, ba sai ya sake yi ba. Ku sanya ido ku gani har zuwa ƙarshen wa’adin lokacin da za mu bar mulki, za mu ci gaba da korar baragurbin mutane da rushe abubuwan da ba su dace ba.”
Gwamnan ya bayyana hakan ne dai kwanaki kaɗan, bayan gwamnatinsa ta soke iznin mallaka na wasu kadarorin tsohon gwamnan jihar, Sanata Ahmed Makarfi, da Kadarorin mallakim mabiya Mazhabar Shi’a, inda ta sanya musu alamar rushewa.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim