Akwai rudani a jam’iyyar PDP kan barazanar da gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed yayi na ficewa daga yaƙin neman zaben Atiku.
An ce gwamnar ya fusata ne kan wasu bayanan sirri da aka samu cewa Alhaji Atiku Abubakar ba ya da sha’awar tsayawa takara a karo na biyu.
An yi zargin cewa ba a ba shi hannu ba don gudanar da yakin neman zabe a Arewa maso Gabas.
Gwamnan ya kuma koka kan yadda dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ya raina shi.
Ya ce a cikin dukkan masu neman takarar shugaban kasa a PDP, shi kadai ne Atiku bai kai ziyara ba domin sasantawa da sulhu.
Haka kuma a jiya, gwamnoni biyar da suka fusata – Nyesom Wike (Rivers), Okezie Ikpeazu (Abia), Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu), Samuel Ortom (Benue) da Seyi Makinde (Oyo) – sun yanke shawarar ci gaba da yaƙin su da Atiku da shugaban ƙasa Iyorchia Ayu.
ALFIJIR HAUSA ta tattaro cewa Mohammed ya zabi ya kasance mai kau da kai ga kwamitin yakin neman zaben shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, duk da nadin da aka yi masa a matsayin mataimakin shugaban yankin Arewa maso Gabas.
Gwamnan ya yi zargin cewa tun da dan takarar bai aminta da shi ba, zai so ya tsaya a waje.