Babban bankin kasa (CBN) ya soke lasisin bankuna 15 da wasu kanfanoni 9 a Nijeriya.
Babban Bankin Najeriya ya soke lasisin aiki na Bankunan Kamfanoni 132, da sauran su
A cewar wata jarida mai dauke da sa hannun gwamnan babban bankin kasa CBN Godwin Emefiele, hukumomin da abin ya shafa kuma sun gaza cika ko kuma cika sharuddan da aka ba su lasisin.
Emefiele ya soke lasisin ne a matsayin ikon da aka bai wa babban bankin Najeriya a karkashin sashe na 12 na BOFIA 2020, doka mai lamba 5.
Bankunan microfinance sun hada da Atlas Microfinance Bank, Bluewhales Microfinance Bank, Everest Microfinance Bank; Mainsail Microfinance Bank; Nopov Microfinance Bank; Premium Microfinance Bank da Stateman Microfinance Bank, Igangan Microfinance Bank, Merit Microfinance Bank, da Minna Microfinance Bank.
Sauran sun hada da Igangan Microfinance Bank, Ohon Microfinance Bank; Zikado Microfinance Bank and Taraba Microfinance Bank.
Babban bankunan jinginar gidaje da abin ya shafa sun hada da Resort Savings & Loans, Safetrust Mortgage Bank, Adamawa Savings & Loans da Kogi Savings & Loans.
Kamfanonin kudi da aka soke lasisin su ne HHL Invest & Trust Limited, TFS Finance Limited da Treasures & Trust Limited.