Babban lauya ya shigar da kara kan a cire nijeriya daga kasashen musulmin duniya.
A watan daya gabata ne wani babban lauya mai suna Malcom Omirhobo, ya shigar da kara domin neman a cire nijeriya daga cikin kasashen musulmi.
Lauyan mai ra’ayin kare ‘yancin dan adam ya shigar dagwamnatin tarayya kara yana neman kotu ta haramtawa cigaba da kasancewa namba a kungiyan kasashe ta duniya wato OIC (Organisation of Islamic Countries).
Lauyan mai suna Malcom Omirhobo, ya nemi babban kotun tarayya dake Abuja ta kuma haramta ma duka jahohi 36 na nijeriya dake Abuja daga alakanta kansu da wani addini ko nuna fifiko kan wani addini ko bin tsarin wani addini a hukumance a jahohin musamman na yankin kudu.
Lauyan ya kara da cewa, nijeriya kasa ne ta kowa da kowa wacce ke dauke da mutane fiye da 200, dake bin addinai da al’adu daban-daban don haka zamewan nijeriya a matsayin mamba a kungiyan kasashen musulmi ya saba dokan kasa.
Sannan tamkar nuna ma duniya ne cewa nijeriya kasan musulmi ne.
A cewan lauyan, ya nemi kotu ta haramta ma nijeriya cigaba da kasancewa OIC, ko bayar da wani tallafi ko guddumawa daga baitul malin kasan zuwa kungiyan ta OIC.
Rahoto Hajiya Mariya Azare.