An kama mataimakin shugaban ƙasar Malawi kan badaƙalar dala 280,000.
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasar Malawi ta ce ta kama mataimakin shugaban ƙasar Saulos Chilima tare da tuhumarsa da laifin badaƙalar cin hanci da ta shafi wani ɗan kasuwa ɗan ƙasar Malawi da kasar Burtaniya.
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ce mataimakin shugaban ƙasar – wanda aka tsige – an tuhume shi da laifuffuka da dama na cin hanci da rashawa da karbar cin hanci don yin tasiri a kan kwangilolin gwamnati.
Kakakin ACB, Egrita Mdala, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, “Ya sami riba ta hanyar kuɗaɗen da suka kai dala 280,000 da sauran kayayyaki daga (ɗan kasuwan Burtaniya-Malawi) Zuneth Sattar,” don kamfanonin na karshen da za a ba su kwangilolin gwamnatin Malawi.
A ranar Juma’a da yamma ne dai Chilima zai gurfana a gaban kotu. Tuni dai jami’ai da magoya bayan jam’iyyarsa ta “United Transformation”/ Movement” suka hallara a waje domin nuna goyon baya.
Shugaba Lazarus Chakwera ya kwace wa Chilima daga karagar mulki a watan Yuni lokacin da aka fara samun cikakken bayani kan zargin satar kuɗin.
A cewar kundin tsarin mulkin Malawi, shugaban kasa ba zai iya dakatarwa ko cire Chilima ba saboda shi zabaɓɓen jami’in ne.
Tuni dai aka kama wasu ministoci da tsaffin ministoci a cikin lamarin, inda aka zargi jami’an gwamnati 53 da karbar kuɗi daga hannun Sattar tsakanin Maris da Oktoban 2021.
Chilima ya yi haɗin gwiwa da Chakwera domin sake lashe zaɓen shugaban ƙasa a shekarar 2020, inda ya kai ga nasara kan wani dandalin yaƙi da cin hanci da rashawa.
Ya kuma bi sahun Chakwera wajen kalubalantar maguɗin zabe a 2019, wanda ya kai ga zaben da kotu ta amince da shi a shekara mai zuwa inda Chakwera ya doke tsohon shugaban kasar Peter Mutharika.
Rahoto: Shamsu A Abubakar Mairiga.