Badaƙalar Murɗe zaɓe na Takarar Gwamnan Bauchi Gwamna Bala yayi Fashin Baƙi.
Nayi alƙawarin bazamu murɗe zaɓen ba zamu bada izinin jama’a suyi Nasara.
Gwamna Bala Muhammad ya roki masu zabe dasu goyi bayan sake zabenshi da kuma dukkan ‘yan takara sauran jam’iyyu a yayin babban zabe.
Yace, nayi alkawarin bazamu murde zaben ba zamu bada izini jama’a suyi nasara inji gwamnan bauchi.
Ina rokonku da ku karbi duk ‘yan siyasan da sukazo wurin yakin neman zabe kada ku gudu domin ku ubanni ne ga kowa.
Bala Muhammad yayi wannan roko ne a lokacin da yake kaddamar da yakin zabenshi a karaman hukuman Itas Gadau da ke jahan Bauchi.
Gwamnan wanda yayi alkawarin cewa, bazai tsoma baki a harkokin zabe, ko musgunawa ko kuma tsoratar da kowa a lokacin zaben.
Ya bayyana kwarin gwiwan cewa ayyukan alheri da yayi a wa’adinshi na farko su zasuyi magana akan shi.
Yace,muna neman goyon bayanku tunda kunga mu masu cika alkawarine a duk lokacin da muka dauka.
Rahoto Hajiya Mariya Azare.