Uwargidan dan takaran shugaban kasa a jam’iyyan PDP, Titi Atiku Abubakar ta bayyana cewa, bai kamata ‘yan Nijeriya suki yarda da ra’ayin mijinta Atiku Abubakar na zama shugaban kasa ba sabida kabilan shi.
Ta bayyana haka ne ranan laraba da ta gabata yayin gangamin yakin neman zaben jam’iyya da aka gudanar a filin shakatawa na damokaradiyya a jahan indo.
Tace, idan Atiku ya zama shugaban kasa tabbas nijeriya zatafi yadda take a yanzu, munci zaben da ya gabata amma an tabka magudi a rumfunan zabe.
Titi tace, gaskiya Atiku bafulatani ne amma ba bafulatanin daji ba ne don yanada wayewa nakasance tare da shi sama da shejaru 40.
A zamanin Obasanjo, Atiku ya tara abubuwa mafi kyawu ga gwamnati, duk yarbawa Atiku naku ne kuma shine zaikawo ci gaban kasarnan.
Idan na zama matan shugaban kasa, zan kula da yara da matasa za’a bada tallafin karatu ku zabi Atiku saboda yasan hanya akwai yunwa a cikin kasa.
Rahoto: Hajiya Mariya Azare.