Bankin Larabawa Ta Sanya Hannu Don Haɓaka Ci gaban Tattalin Arzikin Borno.
Babban Darakta Janar na bankin Larabawa mai kula da ci gaban tattalin arziki a Afirka, Dokta Sidi Ould-Tah ya jaddada ƙudirin bankin na yin haɗin gwiwa da gwamnatin jihar Borno domin bunƙasa tattalin arziki.
Ya bayyana hakan ne a ƙarshen mako a wata ziyarar ban girma da ya kai wa Gwamna Babagana Umara Zulum a Maiduguri.
Ould-Tah, wanda ya jagoranci tawagar bankin zuwa Maiduguri, ya ce haɗin gwiwar da ke da amfani ga bangarorin ya faro ne a shekarar da ta gabata lokacin da gwamnan ya jagoranci tawagar bankin a birnin Khartoum.
“Bankin ya kuma aika da tawagar kwararru zuwa Borno waɗanda suka yi aiki tare da takwarorinsu a nan don shirya aikin gwaji da ake yi a Borno.
“Daga tattaunawar da muka yi da gwamna, muna buƙatar mu ƙara kaimi domin samun damar biyan bukatun al’ummar Borno.
“Kuma wannan shine dalilin da ya sa a yau mun zo nan don tattaunawa da gwamnati game da cikakken shirin bunƙasa karkara don tallafawa jihar Borno,” in ji shi.
A cewarsa, aikin zai kasance mai girma da maƙudan kuɗaɗe daga bankin na tsawon shekaru uku zuwa biyar masu zuwa. Ya ce shirin zai shafi dukkan yankunan da gwamnatin Borno ta tantance.
Da yake mayar da martani, Zulum wanda ya yaba da shiga tsakani da bankin ya yi, ya ce hakan zai sauƙaƙa hanyoyin farfaɗo da tattalin arziki a Borno da yankin kudu da hamadar Sahara.
RAHOTO:- Comrade Yusha’u Garba Shanga.