Batun Sauyin kuɗi: Za’a gurfanar da Shugaban kwamitin bankuna gaban Majalisar Dokoki.
Daga Janaidu Ahmadu Doro.
Za mu gurfanar da shugaban kwamitin Bankuna a gabanmu kan batun sauyin kudade in ji majalissar Dokokin Najeriya.
A wani yunkuri na Daukar Matakin Gaggawa kan batun sauyin kudi majalissar Dokokin Najeriya ta Umurci shugaban kwamitin Bankuna da ya gurfana a gabanta a Gobe Laraba.
A wani zama da majalisar ta yi a yau Talata, ta yanke shawarar gayyato bankunan domin su zo gabanta su yi bayani kan matsalolin ƙarancin kuɗi da ake samu daga Babban Bankin Najeriya, inda daga baya za ta gayyato shuwagabannin CBN domin zuwa su amsa tambayoyi.
Majalissar Dokokin Najeriya ta gayyaci shuagabannin bankunan kasuwanci domin bayyana a gabanta a gobe Laraba kan karancin sabbin takardun kuɗi da ake fuskanta.
Babban Darakta kuma Shugaban Bankunan karkashin kwamitin bankuna, za su haɗu da kwamitin wucin gadi na Majalissar da shugaban masu rinjaye na majalisar Alhassan Ado-Doguwa ke jagoranta.
Majalisar ta kuma bukaci da yi gaggawar tsawaita wa’adin amfani da tsaffin takardun kuɗi zuwa nan da watanni shida.