Bayern Munich na aiki kan jiki kan karfi, domin siyo dan wasan Tottenham, mai kai hari na Ingila Harry Kane, mai shekara 29, karkashin yarjejeniyar da ka iya kai wa yuro miliyan 80 zuwa yuro miliyan 100. (Sky Sports Germany)
Tottenham kuwa na tuntubar Inter Milan kan dan wasanta da Denmark Denzel Dumfries mai shekara 26. (90min)
Ana tababar makomar mai tsaron ragar Senegal Edouard Mendy, dan shekara 30, da dan wasan Sifaniya Kepa Arrizabalaga, mai shekara 28, a Chelsea, a daidai lokacin da kulub din ke duba yiwuwar kawo sabbin ‘yan wasa musamman mai tsaron raga a kakar wasa da ke tafe. (Sun)
Mai kungiyar Bayern Munich Oliver Kahn, ya ce kulub din ba zai dauko dan wasan gaba na Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 37, a watan Janairu ba bayan ficewarsa daga Manchester United. (Sky Germany, via Mirror)
Kahn ya koma kulub din Bundesliga zai yi zama na musamman tare da dan wasan gaba na Kamaru Eric Maxim Choupo-Moting, mai shekara 33, domin tattaunawa kan sabuwar yarjejeniya bayan kammala gasar cin kofin duniya, daidai lokacin da kwantiraginsa zai kare a karshen kakar nan. (Fabrizio Romano)
Roma ta shirya tsaf domin dauko mai kai hari na Ingila Tammy Abraham dan shekara 22 a kakar nan. (Calciomercato – in Italian)
Dan wasan gaba na Argentina da Paris St-Germain Lionel Messi, mai shekara 35, ya na sa ran ci gaba da zama a kulub dinsa har zuwa shekarar 2024, duk da rade-radin wai ya kusan kammala yarjejeniyar komawa kungiyar Inter Miami ta Amurka a badi. (Sky Sports)
Tsohon dan wasan tsakiya na Ingila Joe Cole, ya ce manyan kulub-kulub za su fara rubibin dan wasan Netherland, kuma na tsakiyar PSV Cody Gakpo, mai shekara 23, bayan nasarar da ya kai kasarsa a gasar cin kofin duniya ta 2022 da ke gudana a kasar Qatar. (ITV, via TalkSPORT)
Tsohon shugaban Sheffield United Chris Wilder, na sha’awar cike gurbin aikin Queens Park Rangers ke da shi, bayan Michael Beale ya sauka daga mukamin. (Sun)
Inter Milan na duba yiwuwar dauko dan wasan Barcelona kuma na tsakiyar Ivory Coast Franck Kessie, mai shekara 25, a kaka mai zuwa. (Calciomercato – in Italian)
West Ham kuwa tuni ta shaidawa dan wasan tsakiya na Ireland Conor Coventry, mai shekara 22, ya fara neman sabon aiki gabanin bude kasuwar saye da siyar da ‘yan was a watan Janairu. (Football Insider)
Bayern Munich za ta sayo Kane, ta kuma ce ba za ta sayo Ronaldo ba
Bayern Munich na aiki kan jiki kan karfi, domin siyo dan wasan Tottenham, mai kai hari na Ingila Harry Kane, mai shekara 29, karkashin yarjejeniyar da ka iya kai wa yuro miliyan 80 zuwa yuro miliyan 100. (Sky Sports Germany)
Tottenham kuwa na tuntubar Inter Milan kan dan wasanta da Denmark Denzel Dumfries mai shekara 26. (90min)
Ana tababar makomar mai tsaron ragar Senegal Edouard Mendy, dan shekara 30, da dan wasan Sifaniya Kepa Arrizabalaga, mai shekara 28, a Chelsea, a daidai lokacin da kulub din ke duba yiwuwar kawo sabbin ‘yan wasa musamman mai tsaron raga a kakar wasa da ke tafe. (Sun)
Mai kungiyar Bayern Munich Oliver Kahn, ya ce kulub din ba zai dauko dan wasan gaba na Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 37, a watan Janairu ba bayan ficewarsa daga Manchester United. (Sky Germany, via Mirror)
Rahoto: Ja’afar Muhammad Alkali