Boko haram sun dasa bam da sabbin kudi a garin dauka mutum 2 sun mutu Borno.
Akalla mutane biyu ne suka mutu sakamakon fashewar wasu abubuwa a Damboa daya daga cikin kananan hukumomi 27 dake jihar Borno.
Wata majiyar tsaro da ta bayyana hakan ga majiyar Yola 24 ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 12:00 na daren yau.
Ya ce wasu ‘yan ta’addan da ake zargin ‘yan Boko Haram ne suka tayar da bam din da ke kewayen Dogon Waya, a kan hanyar Damboa zuwa Maiduguri.
Fashewar ta kashe mutane biyu: wani karamin yaro da ya fada tarkon ‘yan ta’addan, wanda aka datsa bam din da takardar kudi naira 200 domin yaudarar mutum.
sai kuma wani mutum wanda yayi kokarin ceto da gawar yaron bam ta sake fashe da shi.
‘Abin takaicin ya faru ne a jiya a lokacin da wani matashi ya ga takardar kudi Naira 200 a bakin titi kuma ana cikin daukar ta ne bam na farko ya tashi tare da shi, inda nan take ya mutu.
Majiyar ta kara da cewa, “Wani mutumin da ya yi yunkurin kwashe gawar yaron ya ci karo da wata bama-bamai kuma daga karshe ya mutu.”
Ya ce wata motar sojoji ta Mine Resistant Ambush Protected ita ma ta fashe lokacin da ta taka wani bam a gefen hanya a wani lamari na daban da ke kusa da axis.