Yaran Nijeriya miliyan 20 da basu zuwa makaranta Ƴan boko haram zasu zama nan gaba.
Yaran da basu zuwa makaranta sun kai miliyan 20.2 ƙarƙashin shugabancin Muhammadu Buhari.
“Tsohon shugaban kasar Nijeriya Cif Olesegun Obasanjo ya koka da yadda ake samun ƙaruwan yaran da basu zuwa makaranta a Nijeriya, yana mai cewa su Ƴan ta’adda ne idan har kasan ta gaza shawo kansu nan gaba.”
Yaran miliyan 20 da basu zuwa makaranta gwamanti zata iya mayar dasu makaranta inji Mista Obasanjo, yace idan bata mayar da su makaranta ba muna shirin tunkaran boko haram gobe zai faru kamar hasken rana.”
“Tsohon shugaban kasan ya bayyana haka ne a wajen taron ƙasa kan sake fasalin makarantun gaba da sakandare da majalisan wakilai ta shirya a abuja ranan talata.
Rahoton yace, Nijeriya ta wuce ƙasan Habasha mai yara miliyan 10.5 da basu zuwa makaranta, Congo nada miliyan 5.9, Kenya nada miliyan 1.8.
“Tsohon shugaban kasar ya cigaba da bayyana irin rashin jin daɗinsa ganin yadda Nijeriya ke fama da ta’addanci a halin yanzu haka, kuma gashi yaran da basu zuwa makaranta sai ƙara nin-ninkuwa suke, bisani sune zasu zama Ƴan ta’adda a nan gaba.
“A cewarsa saboda rashin samun wadataccen ilimi na yara ke kawo yawaitan rashin imani da kuma bushewar idanu duk inji tsohon shugaban kasar.”
Obasanjo, ya ja kunnen Gwamnatin tarayya kan da ta mayar da hankali ganin cewa yaran talakawa sun shiga makaranta, da haka ne zai kawo ƙarancin ta’addanci a Nijeriya.”
Ya kuma ce Harkan ilimi ya fi taɓarbarewa a mulkin Buhari, ganin yadda ilimi ya kasance cikin ƙaƙa-ƙani, na rashin ko inkula a gwamnatance.”
Daga Hajiya Mariya Azare.