Budurwa ta Maka Mahaifinta a kotu sakamakon auren dole da yai Mata a Kaduna.
Wata ‘yarinya a Kaduna ta maka mahaifinta a kotu bisa zargin yi mata auren dole ga wanda ba ta so a zuciyarta.
‘Yarinyar mai suna Fatima ta ce tana da wanda take so a ranta inda ta nemi kotun da ta hana wannan auren
Mai shari’a, Mallam Isiyaku Abdulrahman ya tabbatar da cewa mahaifin nata yana da ‘yancin zaba wa ‘yarsa miji a shari’ance
Wata yarinya ta maka mahaifinta a wata kotu da ke zamanta a Kaduna inda ta roki kotun da ta hana auren dole da yake shirin yi mata.
Yarinyar mai suna Fatima, ‘yar shekara 20 ta bakin lauyanta Mallam Y.A Bulama ta ce tana da wanda take so.
“Mahaifin yarinyar yana son ‘yarshi ta auri wani mutum a kauye cikin jihar Niger, a yanzu haka tana rayuwane a gidan ummarta saboda tilasta mata da mahifin ke son yi na aurar da ita ga wani a kauye.”
Ya kara da cewa ‘yarinyar ba ta yi hakan ba ne don cin mutuncin mahaifinta, Punch.ng ta ruwaito.
Ana shi bangaren, mahaifin ‘yarinyar ya ce iyayensa ne kafun rasuwarsu suka zaba mata miji, kuma dole ya bi umarninsu, kamar yadda rahotannisuka bayyana.
“Na aurar da ‘yata ta shida a kauye kuma suna zaune lafiya, mahaifiyarta ce take zuga ta.”
Mai shari’a, Mallam Isiyaku Abdulrahman ya tabbatar da cewa mahaifin yana da ‘yancin zaba wa ‘yarsa miji a shari’ance.
Ya kara da cewa auren dole ba abu mai kyau bane amma ya bai wa wanda ake karan shawara da ya yi hakuri da ‘yar tasa
Mai shari’a ya ke cewa mahaifinta, ya kamata kayi mata addu’a don samun rayuwa mai kyau, in kana fushi da ita tabbas ba za ta ga abu mai kyau ba”.
“Kabarta ta zabi wanda take so, in yana da addinin da tarbiya, sai ka barta ta aureshi”, in ji shi.
Ya kuma shawarci mai karar da ta kasance ‘ya mai bin umarnin iyayenta.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim.