Buhari ya yi Allah wadai da yadda aka halaka wani basarake a jihar Imo.
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya nuna damuwa game da harin da aka kai kan basaraken gargajiya a jihar Imo.
Wannan na zuwa ne a makon nan bayan da rahotanni suka bayyana yadda ‘yan ta’adda suka farmaki jama’a a Jihar Imo.
Jihar Imo na ɗaya daga jihohin da ‘yan ta’adda suka addaba a ‘yan shekarun nan, ana zargin ‘yan IPOB da barna a yankin Kudu maso Gabas.
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na Najeriya ya bayyana kaɗuwa da samun labarin yadda wasu ‘yan ta’adda suka yiwa basaraken gargajiya, Eze Ignitus Asor na yankin Obudi-Agwa a jihar Imo kisan gilla a makon nan.
Bayan yin Allah-wadai, Buhari ya umarci jami’an tsaro da su gano waɗanda suka aikata wannan mummunan aiki tare da tabbatar da doka a kansu.
Idan baku manta ba, rahoto ya bayyana yadda wasu ‘yan ta’adda suka hallaka basaraken a jihar Imo.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar Buhari ya ce Buhari ya miƙa ta’aziyarsa ga waɗanda suka rasu.
Yayin da yake miƙa ta’aziyya ga iyalai da ‘yan yankin Obudi-Agwa, Buhari ya kuma yiwa wadanda suka raunuka a harin fatan samun lafiya cikin gaggawa.
Hakazalika, ya yaba da kokarin gwamnan jihar Imo wajen haka fannin tsaro tare da karfafawa mazauna jihar gwiwar ci gaba da ba gwamnati hadin kai wajen zakulowa tare da gurfanar da masu aikata laifuka.
Daga Zuhair Ali Ibrahim