Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen bunkasa noma domin bunkasa noma na da darajarsa, domin tabbatar da wadatar abinci a kasar da kuma fitar da kayayyakin amfanin gona zuwa kasashen waje.
Shugaban ya kuma ce a karshen gwamnatin sa zai bar Najeriya cikin hadin kai da wadata da kwanciyar hankali fiye da yadda ya gamu da ita.
Buhari ya bayyana haka ne ta bakin shugaban ma’aikatan fadar sa Farfesa Ibrahim Gambari a wata ziyarar aiki da ya kai don duba matakin aiki a cibiyar bunkasa injinan noma da kayan aikin gona (AMEDI) ranar Lahadin nan a garin Lafia babban birnin jihar Nasarawa.
Shugaban ya ce an dauki manya-manyan matakai na ganin an samu karuwar noma a matsayin daya daga cikin muhimman abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba na sauya fannin daga tsohon tsari zuwa nagartaccen na zamani.
Hakan a cewarsa zai kawo wadatar abinci da tsaro a kasar, da kuma samar da kayayyakin noma zuwa kasashen waje.
Ya kuma yabawa shugabancin hukumar kula da harkokin kimiyya da fasaha ta kasa (NASENI) bisa jajircewa da ci gaban da aka samu kan aikin.
“Shugaban kasa ya bukace ni da in zo nan in duba in ga irin gagarumin ci gaban da ake samu a NASENI, musamman daya daga cikin cibiyoyin bunkasa injinan noma da kayan aiki guda shida.
“Shugaba Buhari yana kallon noma a matsayin wani abu dake da kusanci da zuciyarsa domin yasan cewa lokaci ya yi da za mu samar da abin da za mu ci kuma mu ci abin da muka noma tare da tabbatar da wadatar abinci da tsaron kayan abincin.
“Yana matukar alfahari da kasancewarsa da wannan jiha, yana matukar alfahari da irin gagarumin ci gaban da aka samu a jihar nan, idan Allah ya kaimu zuwa karshen gwamnatinsa zai bar Najeriya cikin hadin kai da wadata da kwanciyar hankali fiye da yadda ya same ta,” inji shi.