Buhari Yayin Bayyana Kadarorinsa, ya ce babu wanda zai tsira a mukarrabansa.
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari umarci dukkan masu madafun iko da su bayyana kadarorinsu
Ya ce tun daga kan mataimakinsa har zuwa kasa babu wanda zai tsira daga bayyana kadarorinsa
Kakakin shugaban, Garba Shehu shi ya bayyana haka a ranar Juma’a 26 ga watan Mayu a Abuja
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana bin doka na bayyana kadarorinsa kafin da kuma bayan ya shiga ofishinsa don inganta aiki da kuma tarbiya a aikin gwamnati.
Kakakin shugaban ne, Mallam Garba Shehu ya bayyana haka a wata sanarwa a ranar Juma’a, ya ce yin hakan zai taimaka wurin yin gaskiya da kuma yaki da cin hanci.
Buhari ya umarci dukkan masu madafun iko da masu mukaman siyasa tun daga kan mataimakin shugaban kasa har kasa da su karbi takardun don cikewa da kuma dawo da shi kamar yadda ya yi, cewar Daily Nigerian.
Da yake magana bayan karbar takardar cikawa daga shugaban hukumar ka’idar aiki da da’a, Farfesa Isah Muhammad a ranar Juma’a, Buhari ya ce babu wanda zai tsira daga bayyana kadarorinsa.
A cewarsa na saka hannu, na karba. Daga nan zan tambayi manajan bankin da nake aiki da shi a Kaduna ya nuna min yanayin shiga da fitar kudi a asusun banki na.
“Babu wanda zai tsira daga bayyana kadarorinsa. Ina so daga mataimakin shugaban kasa ya yi kasa kowa yabi wannan tsarin.”
Mista Mohammed ya ce bin wannan doka da shugaban ya ke yi a shekaru takwas da kuma goyon baya da ya ke bai wa hukumar ya taimaka sun cimma 99% wurin bin doka daga sauran masu mukamai a gwamnati, cewar Punch.
Ya kara da cewa goyon bayan shugaban kasan ya taimaka wa hukumar wurin mai da harkokinta na zamani da kuma binciken matsaloli don aiki yadda ya kamata.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim.