CBN ya bullo da wani tsarin yi wa mutanen karkara canjin tsaffin kudi zuwa sabbi
Daga, Aminu Ahmad
Babban bankin Najeriya CBN ya bullo da wani sabon tsarin yi wa yan Nijeriya musamman mazauna karkara canjin kudi zuwa sabbi a saukake.
Kamar yadda CBN ya fitar da sanarwar canjin kudin a ranar Jumu’a, babban bankin ya ce tsarin zai fara aiki daga ranar Litinin 23 ga watan Janairun 2023
Bankin ya ce za su tura wakilansu a bisa tsarin Deposit Money Bank ‘DMB’ da zai shiga lunguna da sakunan kasar nan don yi wa yan kasar canji musamman ga wadanda ba su da bankuna a yankunan da suke.
Sai dai naira dubu goma N10,000 ce kadai zai iya musanyawa ya bayar da sabbin da aka sauya wa launi na N200, N500 ko N1000, ko kudaden da suke halattatu da ba a canza su ba wato N100 da N50 da N20 har zuwa N5 a ba mutum su idan ya ce wajen yan canjin.
Haka kuma CBN din ya kara da cewa kudaden da suka haura Naira dubu goma N10,000 kuwa za a karba a canza maka amma ba za a baka kudi kasa ba, sai dai a tura maka ta asusun ajiyarka na banki, ga wadanda ba su da asusun ajiyar kuwa, za a bude masu asusun ajiyar na wallet account, a zuba masu kudaden nasu a can.
Dadin dadawa babban bankin ya bayyana cewa ‘agents’ dinsa da ya turo su kadai ne ya aminta da su da su yi wannan aikin musayar kudaden ga wadanda ba za su iya zuwa banki ba, sannan kuma bankin ya haramta amsar ko kwabo a wajen kwastomomin da za a yi wa canjin.
Za a iya tuna cewa babban bankin ya bayyana cewa daga ranar 31 ga wannan watan na Janairu zai rufe amsar tsaffin kudin N1000 da N500 da kuma N200 sai sabbin da ya sauya wa launi.
Miye ra’ayinku